SheTrades Knowledge

Insights and resources for women entrepreneurs, corporates, agricultural stakeholders & policymakers
December 4, 2025

Kasuwanci A TsallakenIyakokin ƙasa da ƙasa:Jagorar kasuwancidon mata a kasuwanninkayan gona naYammacin Afirka


Wannan ƙaramin littafi an yi shi ne don mata masu yin ƙaramin kasuwancin kayan abinci da kayan gona  a tsallaken iyakokin ƙasa da ƙasa a Afirka ta Yamma. Littafin yana bayar da jagoranci a bayyane kuma a aikace don taimaka wa mata su fahimci dokoki da tsare-tsare na harkokin kan iyaka, su gane hukumomi na ƙwarai, su kuma bi dokokin kasuwanci.

Mata da yawa sukan fuskanci munanan yanayi na rashin tsaro ko tauye haƙƙi a kan iyakokin ƙasa da ƙasa. Wannan ƙaramin littafi ya yi bayani a kan irin abubuwan da za a iya farawa da yadda za a shirya musu da kuma wurin da za a sami taimako. Littafin ya ƙunshi sassa guda biyar: rawar da ƙaramin kasuwanci na tsallaken iyakokin ƙasa da ƙasa yake takawa a nahiyar; sanannun hanyoyin shiga da fita na kasuwanci da ma’aikatn hukumomin kan iyakoki; dokokin kasuwanci na wannan nahiya da kayan aiki; yadda za a hana aukuwar karɓar rashawa da tozarci da kuma kai rahoton su; da kuma yadda za a gudanar da kasuwanci cikin aminci kuma bisa tsarin hukuma.

A littafin an yi amfani da sahihan labarai waɗanda suka faru da aka ji daga mata ‘yan kasuwa da jami’an hukumomi masu aiki a kan iyakoki. An nuna yadda kyawawan bayanai da ingantaccen tsari kan iya sa a yi kasuwanci lafiya cikin amimci, ga babu tsangwama, sannan kuma mata su iya ƙimanta gudanar da kasuwanci a tsallaken iyakokin ƙasa da ƙasa na wannan nahiya.
Pages: 88
Size: 13 MB

About the ECOWAS Agricultural Trade (EAT) Programme

Within the framework of the EAT programme, ITC implements a multi-level and multi-stakeholder strategy, closely collaborating with the ECOWAS Commission, Member States, civil society, the private sector, and various trade entities. This holistic approach addresses the political, economic, gender, climate, food, and nutrition security aspects of regional agricultural trade.